Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 7

Warkar da kurma wanda yake kuma bebe

31 Sai Yesu ya bar wajajen Taya, ya bi ta Sidon har zuwa Tekun Galili da kuma cikin yankin Dekafolis.7.31 Wato, Birane Goma 32 A can ne waɗansu mutane suka kawo masa wani kurma, wanda da ƙyar yake magana. Sai suka roƙe shi ɗibiya hannunsa a kan mutumin.

33 Bayan da ya jawo shi gefe, sai Yesu ya sa yatsotsinsa a kunnuwan mutumin, ya tofa miyau ya kuma taɓa harshen mutumin. 34 Ya ɗaga kai sama, ya ja numfashi mai zurfi, sa’an nan ya ce masa, "Effata!" (Wato, "Buɗe!"). 35 Bayan ya faɗa haka, sai kunnuwan mutumin suka buɗe, harshensa kuma ya kunce, sai ya fara magana sarai.

36 Yesu ya umarce su, kada su gaya wa kowa. Amma ƙara yawan kwaɓarsu ƙara yawan yaɗa labarin suke ta yi. 37 Mutane suka cika da mamaki, suka ce, "Kai, ya yi kome daidai. Har ma yana sa kurame su ji, bebaye kuma su yi magana."

Veja também