6 Ya amsa ya ce, "Daidai ne Ishaya ya yi annabci game da ku munafukai; kamar yadda yake a rubuce cewa,
" ‘Waɗannan mutane da baki suke girmama ni,
amma zukatansu sun yi nesa da ni.
7 A banza suke mini sujada,
koyarwarsu, dokokin mutane ne kawai.’ 7.7 Ish 29.13
8 Kun yar da umarnan Allah, kuna bin al’adun mutane."