An warkar da makaho
22 Suka iso Betsaida, sai waɗansu mutane suka kawo wani makaho, suka roƙi Yesu yă taɓa shi. 23 Yesu ya kama hannun makahon ya kai shi bayan ƙauyen. Bayan ya tofa miyau a idanun mutumin, ya kuma ɗibiya masa hannuwansa, sai ya tambaye shi ya ce, "Kana iya ganin wani abu?"
24 Sai ya ɗaga kai ya ce, "Ina ganin mutane, suna kama da itatuwa da suke tafiya."
25 Yesu ya sāke ɗibiya hannuwansa a idanun mutumin, sai idanunsa suka buɗe, ya sami gani, ya kuma ga kome sarai. 26 Yesu ya sallame shi gida ya ce, "Kada ka shiga cikin ƙauyen."8.26 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Kada ka faɗa wa kowa a ƙauyen