Pular para o conteúdo
Publicidade

Marcos 9

17 Wani mutum a cikin taron ya amsa ya ce, "Malam, na kawo maka ɗana mai wani ruhun da yake hana shi magana. 18 Duk lokacin da mugun ruhun ya kama shi, yakan jefa shi a ƙasa. Bakinsa yakan yi kumfa, cije haƙorarsa, yakan sa jikinsa ya sandare, zama da ƙarfi. Na roƙi almajiranka su fitar da ruhun, amma ba su iya ba."

19 Yesu ya ce, "Ya ku zamani marar bangaskiya, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron."

20 Sai suka kawo shi. Da ruhun ya ga Yesu, nan da nan sai ya buge yaron da farfaɗiya. Ya fāɗi a ƙasa, yana birgima, bakinsa yana kumfa.

21 Yesu ya tambayi mahaifin yaron ya ce, "Tun yaushe yake haka?"

Ya ce, "Tun yana ƙarami. 22 Ya sha jefa shi cikin wuta, ko ruwa don kashe shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu."

23 Yesu ya ce, " In za ka iya? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata."

24 Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, "Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!"

25 Da Yesu ya ga taron suna zuwa can a guje, sai ya tsawata wa mugun ruhun ya ce, "Kai ruhun kurma, da na bebe, na umarce ka, ka fita daga cikinsa, kada kuma ka ƙara shigarsa."

26 Sai ruhun ya yi ihu, ya buge shi da ƙarfi da farfaɗiya, ya fita. Yaron ya kwanta kamar matacce, har mutane da yawa suka ce, "Ai, ya mutu." 27 Amma Yesu ya kama shi a hannu ya ɗaga, ya kuwa tashi tsaye.

Veja também