Pular para o conteúdo
Publicidade

Mattiyu 1

Asalin Yesu Kiristi

1 Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.

2 Ibrahim ya haifi Ishaku,

Ishaku ya haifi Yaƙub,

Yaƙub ya haifi Yahuda da yan’uwansa,

3 Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu;

Ferez ya haifi Hezron,

Hezron ya haifi Ram,

4 Ram ya haifi Amminadab,

Amminadab ya haifi Nashon,

Nashon ya haifi Salmon,

5 Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa,

Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa,

Obed ya haifi Yesse,

6 Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda.

Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.

7 Solomon ya haifi Rehobowam,

Rehobowam ya haifi Abiya,

Abiya ya haifi Asa,

8 Asa ya haifi Yehoshafat,

Yehoshafat ya haifi Yehoram,

Yehoram ya haifi Azariya,

9 Azariya ya haifi Yotam,

Yotam ya haifi Ahaz,

Ahaz ya haifi Hezekiya,

10 Hezekiya ya haifi Manasse,

Manasse ya haifi Amon,

Amon ya haifi Yosiya,

11 Yosiya kuma ya haifi Yekoniya1.11 Wato, Jehohiyachin; haka ma a aya 12 da yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.

12 Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon.

Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel,

Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,

13 Zerubbabel ya haifi Abiyud,

Abiyud ya haifi Eliyakim,

Eliyakim ya haifi Azor,

14 Azor ya haifi Zadok,

Zadok ya haifi Akim,

Akim kuma ya haifi Eliyud,

15 Eliyud ya haifi Eleyazar,

Eleyazar ya haifi Mattan,

Mattan ya haifi Yaƙub,

16 Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.

17 Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.1.17 Ko kuwa Kiristi. Kiristi (Da Girik) Almasihu (Da Ibraniyanci) duk suna nufin "Shafaffe."

Veja também