2 Ga sunayen manzannin nan goma sha biyu,
da fari, Siman (wanda ake kira Bitrus) da ɗan’uwansa Andarawus;
Yaƙub ɗan Zebedi da ɗan’uwansa Yohanna;
3 Filibus da Bartolomeyu;
Toma da Mattiyu mai karɓar haraji;
Yaƙub ɗan Alfayus da Taddayus;
4 Siman Zilot da kuma Yahuda Iskariyot wanda ya bashe Yesu.