15 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce, "Wurin nan fa ba kowa, ga shi kuma rana ta kusa fāɗuwa. Ka sallami taron don su shiga ƙauyuka su nemi wa kansu abinci."
16 Yesu ya amsa, "Ba su bukata su tafi. Ku ku ba su wani abu su ci."
17 Suka ce, "Burodi biyar da kifi biyu ne kawai muke da su a nan."
18 Ya ce, "Ku kawo mini su a nan." 19 Sai ya umarci mutanen su zazzauna a kan ciyawa. Da ya ɗauki burodi biyar da kifin biyun nan ya dubi sama, ya yi godiya ya kuma kakkarya burodin. Sa’an nan ya ba wa almajiransa, almajiran kuwa suka ba wa mutane. 20 Duk suka ci suka ƙoshi, almajiran kuwa suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu. 21 Yawan waɗanda suka ci, sun yi wajen maza dubu biyar, ban da mata da yara.