32 Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, "Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya."
33 Sai almajiransa suka amsa suka ce, "Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?"
34 Yesu ya tambaye su, "Burodi guda nawa kuke da shi?"
Suka amsa suka ce, "Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye."
35 Ya sa taron su zazzauna a ƙasa. 36 Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane. 37 Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai. 38 Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.