Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 16

Yistin Farisiyawa da Sadukiyawa

5 Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi. 6 Yesu ya ce musu, "Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa."

7 Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, "Ko don ba mu kawo burodi ba ne."

8 Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, "Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba? 9 Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike? 10 Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? 11 Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa." 12 Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

Veja também