Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 17

Warkarwar yaro mai aljani

14 Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15 Ya ce, "Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16 Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba."

17 Yesu ya amsa ya ce, "Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan." 18 Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

Veja também