Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 17

Harajin haikali

24 Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, "Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne17.24 da Girik darik biyu?"

25 Ya amsa ya ce "I, yana biya."

Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, "Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?"

26 Bitrus ya amsa ya ce, "Daga wurin waɗansu."

Yesu ya ce masa, "Wato, an ɗauke wa ya’yan ke nan. 27 Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan."

Veja também