Mafi girma a mulkin sama
1 A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, "Wane ne mafi girma a mulkin sama?"
2 Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. 3 Sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. 4 Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. 5 Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.
(Markus 9.42-48; Luka 17.1,2)
10 "Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama. 18.10 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da sama. 11 Ɗan Mutum ya zo ne domin yă ceci abin da ya ɓata