Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 2

Ziyarar Masana

1 Bayan an haifi Yesu a Betlehem, a Yahudiya, a zamanin Sarki Hiridus, sai waɗansu Masana,2.1 A al’adance Masu Hikima daga gabas suka zo Urushalima 2 suka yi tambaya suka ce, "Ina shi wanda aka haifa sarkin Yahudawa? Gama mun ga tauraronsa a gabas2.2 Ko kuwa a tauraro sa’ad da ya taso mun kuwa zo ne domin mu yi masa sujada."

3 Da Sarki Hiridus ya ji wannan, sai hankalinsa ya tashi haka ma na dukan Urushalima. 4 Bayan ya kira dukan manyan firistoci da malaman dokoki na mutane wuri ɗaya, sai ya tambaye su inda za a haifi Kiristi. 5 Suka amsa suka ce, "A Betlehem ne, cikin Yahudiya, gama haka annabin ya rubuta.

6 " Amma ke Betlehem, a cikin ƙasar Yahuda,

ba ke ce mafi ƙanƙanta a cikin masu mulki a Yahuda ba,

gama daga cikinki mai mulki zai zo,

wanda zai zama makiyayin mutanena Isra’ila.2.6 Mik 5.2"

7 Sai Hiridus ya kira Masanan nan a ɓoye, gano daga wurinsu daidai lokacin da tauraron ya bayyana. 8 Sai ya aike su Betlehem ya ce, "Ku je ku binciko a hankali game da yaron nan. Da kun same shi, sai ku kawo mini labari nan da nan, domin ni ma in je in yi masa sujada."

9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. 12 Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.

Veja também