9 Bayan sun saurari sarki, sai suka kama hanyarsu, tauraron da suka gani a gabas kuwa yana tafe a gabansu, sai da ya kai inda yaron yake. 10 Da suka ga tauraron, sai suka yi farin ciki ƙwarai. 11 Suka shiga gidan, suka kuwa ga yaron tare da mahaifiyarsa Maryamu. Suka durƙusa har ƙasa, suka yi masa sujada. Sa’an nan suka kunce dukiyarsu, suka miƙa masa kyautai na zinariya da na turare da na mur. 12 Bayan an gargaɗe su cikin mafarki kada su koma wurin Hiridus, sai suka koma ƙasarsu ta wata hanya dabam.