Roƙon mahaifiya
20 Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.
21 Ya yi tambaya ya ce, "Mene ne kike so?"
Ta ce, "Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka."
22 Yesu ya ce musu, "Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?"
Suka amsa, "Za mu iya."
23 Yesu ya ce musu, "Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne."