Makafi biyu sun sami ganin gari
29 Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30 Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, "Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!"
31 Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, "Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!"
32 Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, "Me kuke so in yi muku?"
33 Suka amsa suka ce, "Ubangiji, muna so mu sami ganin gari."
34 Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.