Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 21

Shigar mai nasara

1 Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2 yana ce musu, "Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3 In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan."

4 Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,

5 "Ku ce wa Diyar Sihiyona,

Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,

mai tawali’u yana a kan jaki,

a kan aholaki, ɗan jaki.’ "21.5 Zak 9.9

6 Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7 Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. 8 Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. 9 Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,

"Hosanna21.9 Wani faɗi na Ibraniyanci mai ma’anar "Ceto!" Wanda ya kasance wani salon yabo; haka kuma a aya 15 ga Ɗan Dawuda!"

"Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!"21.9 Zab 118.26

"Hosanna a cikin sama!"

10 Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, "Wane ne wannan?"

11 Taron mutane suka amsa, "Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili."

Veja também