Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 21

Itacen ɓaure ya yanƙwane

18 Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. 19 Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, "Kada ka ƙara yin ya’ya!" Nan da nan itacen ya yanƙwane.

20 Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, "Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?"

21 Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, Je ka, ka jefa kanka cikin teku,sai faru. 22 In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a."

Veja também