Pular para o conteúdo
Publicidade

Mattiyu 22

Aure a tashin matattu

23 A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya. 24 Suka ce "Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ya’ya, dole ɗan’uwansa auri gwauruwar kuma haifar wa ɗan’uwan ya’ya. 25 A cikinmu an yi yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa. 26 Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai. 27 A ƙarshe, macen ta mutu. 28 To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za zama, da yake dukansu sun aure ta?"

29 Yesu ya amsa ya ce, "Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba. 30 Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama. 31 Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne, 32 Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub22.32 Fit 3.6? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne."

33 Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.

Veja também