29 "Nan da nan bayan tsabar wahalan nan
" ‘sai a duhunta rana,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,
za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’ 24.29 Ish 13.10; Ish 34.4
30 "A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma.