Publicidade

Mateus 25

36 da nake bukatar tufafi, kun yi mini sutura, da na yi rashin lafiya, kun lura da ni, da nake kurkuku, kun ziyarce ni.

37 "Sa’an nan masu adalci za su amsa masa, su ce, Ubangiji, yaushe muka gan ka da yunwa muka ciyar da kai, ko da ƙishirwa muka ba ka abin sha? 38 Yaushe kuma muka gan ka baƙo muka karɓe ka, ko cikin bukatar tufafi muka yi maka sutura? 39 Yaushe kuma muka gan ka cikin rashin lafiya ko a kurkuku muka ziyarce ka?

40 "Sarkin zai amsa ya ce, Gaskiya nake gaya muku, duk abin da kuka yi wa ɗaya daga cikin waɗannan yan’uwana mafi ƙanƙanta, ni kuka yi wa.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-