Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 26

An ƙulla shawara gāba da Yesu

1 Sa’ad da Yesu ya gama faɗin dukan waɗannan abubuwa, sai ya ce wa almajiransa, 2 "Kamar yadda kuka sani, Bikin Ƙetarewa sauran kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum don a gicciye shi."

3 Sai manyan firistoci da dattawan mutane, suka taru a fadan babban firist, mai suna Kayifas, 4 suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci, su kuma kashe shi. 5 Suka ce, "Amma ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su da rikici."

An shafe Yesu a Betani

6 Yayinda Yesu yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, 7 wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tulun alabasta na turaren mai tsada sosai, wanda ta zuba a kansa a lokacin da yake cin abinci.

8 Sa’ad da almajiransa suka ga wannan, sai suka yi fushi. Suka ce, "Wannan almubazzaranci fa! 9 Wannan turare ai, da an sayar da shi da kuɗi mai yawa a ba matalauta kuɗin."

10 Sane da wannan, Yesu ya ce musu, "Me ya sa kuke damun macen nan? Ta yi mini abu mai kyau ne. 11 Matalauta za su kasance tare da ku kullum, amma ni ba zan kasance tare da ku kullum ba. 12 Sa’ad da ta zuba turaren nan a jikina, ta shirya ni ne don jana’izata. 13 Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bisharan nan a duniya duka, abin da matan nan ta yi, za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita."

Yahuda ya yarda bashe Yesu

14 Sai ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, wanda ake kira Yahuda Iskariyot, ya je wurin manyan firistoci 15 ya ce, "Me za ku ba ni, in na bashe shi gare ku?" Sai suka ƙirga masa kuɗi azurfa talatin. 16 Daga wannan lokaci, Yahuda ya yi ta neman zarafin da zai miƙa shi.

Abincin yamma na Ubangiji

17 A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, sai almajiran suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, "Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?"

18 Ya amsa ya ce, "Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, Malam ya ce, lokacina ya yi kusa. Zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina a gidanka.’ " 19 Saboda haka almajiran suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka kuwa shirya Bikin Ƙetarewa.

20 Da yamma ta yi, sai Yesu ya zauna don cin abinci tare da Sha Biyun. 21 Yayinda suke cin abinci, sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni."

22 Suka yi baƙin ciki ƙwarai, suka fara ce masa da ɗaya-ɗaya, "Gaskiya nake gaya muku, ɗayanku zai bashe ni."

23 Yesu ya amsa ya ce, "Wanda ya sa hannunsa a kwano tare da ni ne, zai bashe ni. 24 Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda aka rubuta game da shi. Amma kaiton mutumin da zai bashe Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da ya fi masa."

25 Sa’an nan Yahuda, wanda zai bashe shi ya ce, "Tabbatacce ba ni ba ne, ko, Rabbi?"

Yesu ya amsa ya ce, "I, kai ma ka fada."26.25 Ko kuwa "Kai kanka ka faɗa"

26 Yayinda suke cikin cin abinci, Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya ya kuma kakkarya, ya ba wa almajiransa yana cewa, "Ku karɓa ku ci; wannan jikina ne."

27 Sa’an nan ya ɗauki kwaf, ya yi godiya, ya kuma ba su, yana cewa, "Ku shassha daga cikinsa, dukanku. 28 Wannan jinina ne na sabon alkawari, wanda aka zubar saboda mutane da yawa, don gafarar zunubai.

Veja também