18 Sai Yesu ya zo wurinsu ya ce, "An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19 Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin28.19 Ko kuwa cikin; dubi Ayy M 8.16; 19.5; Rom 6.3; 1Kor 1.13; 10.2 da Gal 3.27 sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, 20 kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani."
Publicidade