Pular para o conteúdo
Publicidade

Mattiyu 3

Yohanna Mai Baftisma ya shirya hanya

1 A waɗancan kwanaki, Yohanna Mai Baftisma ya zo, yana wa’azi a Hamadan Yahudiya 2 yana cewa, "Ku tuba, gama mulkin sama ya yi kusa." 3 Wannan shi ne wanda aka yi maganarsa ta wurin annabi Ishaya cewa,

"Ga murya mai kira a hamada tana cewa,

Ku shirya wa Ubangiji hanya,

ku miƙe hanyoyi dominsa.’ "3.3 Ish 40.3

4 Tufafin Yohanna kuwa an yi su da gashin raƙumi ne, yana kuma daure da ɗamara ta fata. Abincinsa kuwa fāri ne da zumar jeji. 5 Mutane suka zo wurinsa daga Urushalima da dukan Yahudiya da kuma dukan yankin Urdun. 6 Suna furta zunubansu, ya kuma yi musu baftisma a Kogin Urdun.

Veja também