Gwajin Yesu
1 Sa’an nan Ruhu ya kai Yesu cikin hamada don Iblis yă gwada shi. 2 Bayan ya yi azumi yini arba’in da kuma dare arba’in, sai ya ji yunwa. 3 Sai mai gwajin ya zo wurinsa ya ce, "In kai Ɗan Allah ne, ka ce wa duwatsun nan su zama burodi."
4 Yesu ya amsa ya ce, "A rubuce yake cewa, ‘Ba da abinci kaɗai mutum yake rayuwa ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga bakin Allah.’4.4 M Sh 8.3"
5 Sai Iblis ya kai shi birni mai tsarki, ya kai shi can wuri mafi tsayi duka na haikali. 6 Ya ce, "In kai Ɗan Allah ne, yi tsalle ka sauka ƙasa. Gama a rubuce yake,
" ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai,
za su tallafe ka da hannuwansu,
don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’4.6 Zab 91.11,12"
7 Yesu ya amsa masa ya ce, "A rubuce yake kuma cewa, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’4.7 M Sh 6.16"
8 Har wa yau, Iblis ya kai shi bisa wani dutse mai tsawo sosai, ya nunnuna masa dukan mulkokin duniya da darajarsu. 9 Ya ce, "Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada."
10 Sai Yesu ya ce masa, "Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’4.10 M Sh 6.13"
11 Sa’an nan Iblis ya bar shi, mala’iku kuwa suka zo suka yi masa hidima.