Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 5

Ƙauna don abokan gāba

43 "Kun dai ji an faɗa, Ka ƙaunaci maƙwabcinka, 5.43 Fir 19.18 ka kuma ƙi abokin gābanka. 44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku5.44 Waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba suna da abokan gāba, ku sa wa waɗanda suke la’antarku albarka, ku yi wa waɗanda suke ƙinku alheri kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci. 46 In masoyarku kawai kuke ƙauna, wace lada ce gare ku? Ko masu karɓar haraji ma ba haka suke yi ba? 47 In kuwa kuna gai da yan’uwanku ne kaɗai, me kuke yi fiye da waɗansu? Marasa bin Allah ma ba haka suke yi ba? 48 Saboda haka sai ku zama cikakku, yadda Ubanku na sama yake cikakke.

Veja também