44 Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku5.44 Waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba suna da abokan gāba, ku sa wa waɗanda suke la’antarku albarka, ku yi wa waɗanda suke ƙinku alheri kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a, 45 don ku zama ’ya’yan Ubanku na sama. Shi yakan sa ranarsa ta haskaka a kan mugaye da masu kirki; yakan kuma sako ruwan sama a bisa masu adalci da marasa adalci.