Bayarwa ga mabukata
1 "Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.
2 "Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 3 Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, 4 don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.
Addu’a
(Luka 11.2-4)
6 Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.