Publicidade

Mateus 6

Kada ku damu

25 "Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26 Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27 Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya?

Veja também

Publicidade
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-06-28_14-13-17-