Pular para o conteúdo
Publicidade

Mateus 8

Yesu ya kwantar da hadari

23 Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24 Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25 Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, "Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!"

26 Ya amsa ya ce, "Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?" Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

27 Mutanen suka yi mamaki suka ce, "Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!"

Veja também