2 Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, "Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka."
3 Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, "Wannan mutum yana yin saɓo!"
4 Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, "Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? 5 Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ 6 Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai." Sai ya ce wa shanyayyen, "Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida." 7 Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.