Pular para o conteúdo
Publicidade

Nehemiya 4

Hamayya ga sāke ginin

1 Da Sanballat ya ji cewa muna sāke ginin katangar, sai ya husata, ya haukace ƙwarai. Ya yi wa Yahudawa dariya, 2 a gaban abokansa da kuma sojojin Samariya ya ce, "Me waɗancan Yahudawan nan marasa ƙarfi suke yi? Za su maido da katangarsu ne? Za su miƙa hadayu ne? Za su gama a rana ɗaya? Za su iya samun duwatsun gini daga tsibin matattun duwatsu?"

3 Tobiya wakilin mutanen Ammon wanda yake a gefensa ya ce, "Abin nan da suke gini, ko dila ma ya hau, zai rushe shi!"

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também