Ribar ɗa’ar hikima
1 Ɗana, in ka yarda da kalmomina
ka kuma ajiye umarnaina a cikinka,
2 kana kasa kunne ga abin da yake na hikima,
kana kuma yin ƙoƙari ka fahimce shi,
3 in kuma ka kira ga tsinkaya
ka kuma kira da ƙarfi don ganewa,
4 in ka neme shi yadda ake neman azurfa
ka kuma neme shi kamar yadda ake neman ɓoyayyiyar dukiya,
5 to, za ka gane tsoron Ubangiji
ka kuma sami sanin Allah.
6 Gama Ubangiji yana ba da hikima,
daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.