9 Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya,
gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
10 Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,
kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,
gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.