Pular para o conteúdo
Publicidade

Provérbios 5

15 Ku sha ruwa daga tankinku,

ruwa mai gudu daga rijiyarku.

16 In maɓulɓulanku suka cika suna malala har waje,

rafuffukan ruwanku a dandalin jama’a?

17 Bari su zama naka kaɗai,

don kada ka raba da baƙi.

18 Bari maɓulɓulanka ya zama mai albarka,

bari kuma ka yi farin ciki da matar ƙuruciyarka.

19 Ƙaunatacciyar mariri, barewa mai kyan gani,

bari mamanta su ishe ka kullum,

bari ƙaunarta ta ɗauke hankalinka kullum.

20 Ɗana, me ya sa za ka bari mazinaciya ta ɗauke maka hankali?

Don me za ka rungume matar wani?

Veja também