Publicidade

Romanos 14

Marasa ƙarfi da masu ƙarfi

1 Ku karɓi wanda bangaskiyarsa ba yi ƙarfi ba, amma fa kada ku hukunta shi a kan abubuwan da ake da shakka a kai ba. 2 Bangaskiyar mutum ta yarda masa ci kome, amma wanda bangaskiyarsa ba yi ƙarfi ba, yakan ci kayan lambu ne kawai. 3 Mutumin da yake cin kowane irin abinci, kada rena wanda ba ya cin, wanda kuma ba ya cin kowane irin abinci, kada ga laifin mutumin da yake ci, domin Allah ya riga ya karɓe shi. 4 Kai wane ne har da za ka ga laifin bawan wani? Ko bawan yi aiki mai kyau, ko kāsa, ai, wannan ruwan maigidansa ne. Za a ma tsai da shi, domin Ubangiji yana da ikon tsai da shi.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-