Pular para o conteúdo
Publicidade

Romawa 4:17-21

17 Kamar yadda yake a rubuce cewa, "Na mai da kai uban al’ummai masu yawa."4.17 Far 17.5 Shi ubanmu ne a gaban Allah, wanda a cikinsa ya gaskata, Allahn da yake ba da rai ga matattu, yake kuma kiran abubuwan da ba su kasance ba su zama kamar sun kasance.

18 Saɓanin dukan bege, Ibrahim cikin bege ya gaskata, haka kuwa ya zama uban al’ummai masu yawa, kamar yadda aka riga aka faɗa masa cewa, "Haka zuriyarka za tă zama."4.18 Far 15.5 19 Ba tare da ya bar bangaskiyarsa ta yi rauni ba, ya fuskanci gaskiyan nan mai cewa jikinsa mai tsufa matacce ne, da yake yana da shekara wajen ɗari, mahaifar Saratu kuma matacciya ce. 20 Duk da haka bai yi shakka ta wurin rashin bangaskiya game da alkawarin Allah ba, sai ma ya ƙara ƙarfafa ga bangaskiyarsa, ya kuma ɗaukaka Allah, 21 yana kuma da cikakken tabbaci cewa Allah yana da iko yă cika abin da ya yi alkawari.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.