Pular para o conteúdo
Publicidade

Romawa 5:1-5

Salama da farin ciki

1 Saboda haka, da yake an same mu marasa laifi ta wurin bangaskiya, muna5.1 Ko kuwa bari mu da salama tare da Allah ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi, 2 ta wurinsa ne muka sami shiga wannan alherin da muke tsaye yanzu, ta wurin bangaskiya. Muna kuma5.2 Ko kuwa bari mu farin ciki a begen ɗaukakar Allah. 3 Ba haka kawai ba, amma muna5.3 Ko kuwa bari mu kuma da farin ciki cikin shan wuyanmu, gama mun san cewa shan wuyan nan takan haifi jimiri; 4 jimiri kuma yakan kawo hali mai kyau; hali mai kyau kuma yakan sa bege. 5 Bege kuwa ba ya ba mu kunya, domin Allah ya zuba ƙaunarsa a zukatanmu ta wurin Ruhu Mai Tsarkin da ya ba mu.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.