12 Saboda haka kada ku bar zunubi yă mallaki jikin nan naku mai mutuwa yă sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-sha’awacensa. 13 Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci. 14 Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri.
15 Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! 16 Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? 17 Amma godiya ga Allah don ko da yake a dā ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. 18 An ’yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.