Publicidade

Romanos 8

Rai ta wurin Ruhu

1 Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, 2 gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta yantar da ni daga Dokar Musa. 3 Gama abin da dokar ba iya yi saboda kāsawar mutuntaka ba, Allah ya yi shi sa’ad da ya aiko da Ɗansa a kamannin mutum mai zunubi, don zama hadaya ta zunubi. Ta haka, ya hukunta zunubi a cikin mutum mai zunubi. 4 Ya yi haka domin cika bukatun adalcin doka a cikinmu, mu da ba ma rayuwa bisa ga mutuntaka, sai dai bisa ga Ruhu.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-