Fiye da masu nasara
28 Mun kuma san cewa a cikin dukan abubuwa Allah yana aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa,8.28 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da, A cikin dukan al’amura Allah yana8.28 Ko kuwa aikata alheri ga waɗanda suke ƙaunarsa; waɗansu rubuce-rubucen hannu kuma suna da, dukan al’amura suna aikata tare zuwa ga alheri ga masu ƙaunar Allah waɗanda aka kira bisa ga nufinsa. 29 Gama waɗanda Allah ya rigyasani ya kuma ƙaddara su dace da kamannin Ɗansa, don yă zama ɗan fari cikin ’yan’uwa masu yawa. 30 Waɗanda kuwa ya ƙaddara, su ne ya kira; waɗanda ya kira kuwa, su ne ya kuɓutar; waɗanda ya kuɓutar kuwa, su ne ya ɗaukaka.