Pular para o conteúdo
Publicidade

Rut 1

11 Amma Na’omi ta ce, "Ku koma gida, ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ya’ya maza da za su zama mazanku ne? 12 Ku koma gida ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ya’ya maza, 13 za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!"

Veja também

Rute
Ver todos os capítulos de Rute