Pular para o conteúdo
Publicidade

Rute 1

8 Sai Na’omi ta ce wa surukanta biyu, "Ku koma, kowannenku, zuwa gidan mahaifiyarta. Bari Ubangiji nuna muku alheri yadda kuka nuna wa matattun nan da kuma gare ni. 9 Bari Ubangiji sa kowannenku ta sami hutu a gidan wani miji."

Sa’an nan ta sumbace su suka kuma yi kuka da ƙarfi 10 suka ce mata, "Za mu tafi tare da ke zuwa ga mutanenki."

11 Amma Na’omi ta ce, "Ku koma gida, ya’yana mata. Don me za ku tafi tare da ni? Zan ƙara samun waɗansu ya’ya maza da za su zama mazanku ne? 12 Ku koma gida ya’yana mata; na tsufa ainun da zan sāke samun wani miji. Ko ma na yi tsammani har yanzu ina da bege, ko ma na sami miji a wannan dare na kuma haifi ya’ya maza, 13 za ku jira sai sun yi girma? Za ku ci gaba da kasance babu aure saboda su? A’a, ya’yana mata. Ina da baƙin ciki ƙwarai fiye da ku, domin hannun Ubangiji ya yi gāba da ni!"

14 A kan wannan suka sāke ɓarke da kuka. Sa’an nan Orfa ta sumbaci surukarta ta yi bankwana, amma Rut ta manne mata.

Veja também

Rute
Ver todos os capítulos de Rute