14 Mata suka ce wa Na’omi, "Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah yă sa yă zama sananne a dukan Isra’ila! 15 Zai sabunta rayuwarki yă adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da ’ya’ya maza bakwai, ta haife shi."
16 Sai Na’omi ta ɗauki yaron, ta kwantar da shi a cinyarta ta kuma kula da shi. 17 Matan da suke zama a wurin suka ce, "Na’omi ta sami yaro." Suka kuwa ba shi suna Obed. Shi ne ya haifi Yesse, mahaifin Dawuda.