Pular para o conteúdo
Publicidade

Yaƙub 4:4,6-8

4 Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa yă zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan. 6 Amma yakan ba mu alheri a yalwace. Shi ya sa Nassi ya ce,

"Allah yana gāba da masu girman kai

amma yakan ba da alheri ga masu tawali’u."4.6 K Mag 3.34

7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku. 8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.