8 Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu. 9 Ku yi baƙin ciki, ku yi makoki ku kuma yi kuka. Ku mai da dariyarku ta zama makoki, farin cikinku kuma yă zama ɓacin zuciya. 10 Ku ƙasƙantar da kanku a gaban Ubangiji, zai kuwa ɗaukaka ku.
Publicidade