Pular para o conteúdo
Publicidade

Ajuda para casais

Por Bíblia Online

Deus fortalece casamentos. A Bíblia oferece sabedoria prática para casais: comunicar com verdade, perdoar com graça, servir com amor e buscar a Deus juntos.

Amor e respeito

Maridos, amai vossas mulheres. Mulheres, respeitem seus maridos. O amor mútuo edifica o casamento.

Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.

Duk da haka, dole kowannenku ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar yi biyayya ga mijinta.

Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne. Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ciyar da shi, kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,

Saboda haka dole kowannenku bar yin ƙarya, kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.

"Cikin fushinku kada ku yi zunubi." Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi, kada kuma ku ba wa Iblis dama.

Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za zama da amfani ga masu jinta.

Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta. Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

União e fidelidade

O que Deus ajuntou não separe o homem. Eu e minha casa serviremos ao Senhor. A fidelidade é alicerce do casamento.

Ta haka, ba sa ƙara zama biyu, sai dai ɗaya. Saboda haka abin da Allah ya haɗa fa, kada mutum raba."

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Aure zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci.

Umarnai don iyalan masu bi

Mata, ku yi biyayya ga mazanku, yadda ya dace cikin Ubangiji.

Maza, ku ƙaunaci matanku kada ku nuna musu hali marar tausayi.

Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

Ku bar salamar Kiristi yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.

Perdão e paciência

Sede bondosos e compassivos uns com os outros. O amor é paciente, benigno. Permanece e persevera.

Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya. Ƙauna ba ta jin daɗin mugunta, sai dai ta ji daɗin gaskiya. Tana kāriya kullum, tana amincewa kullum, tana bege kullum, tana jimrewa kullum.

Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma saki matarsa.

Ya kamata miji cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku.

Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku. Bai kamata kowannenku kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai kula da sha’anin waɗansu ma.

Ku tabbata cewa kada kowa rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.

Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau

ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.

Seja o primeiro