Amigo
O amigo verdadeiro é dádiva rara de Deus. Ele ama em todo tempo, fala a verdade em amor, aconselha com sabedoria e permanece fiel nas adversidades da vida.
Amizade verdadeira
Há amigo mais chegado que um irmão. Em todo tempo ama o amigo. O perfume e o incenso alegram o coração — assim o conselho doce do amigo.
Mutum mai abokai masu yawa kan lalace,
amma akwai abokin da yakan manne kurkusa fiye da ɗan’uwa.
Aboki yakan yi ƙauna a koyaushe,
ɗan’uwa kuma, ai, don ɗaukar nawayar juna ne aka haife shi.
Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya,
gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.
Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe
haka mutum kan koyi daga mutum.
Gara tsawatawar da ake yi a fili
da ƙaunar da ake yi a ɓoye.
Za a iya amince da rauni daga aboki,
amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!
Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka,
kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka,
gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.
Shi da yake tafiya tare da masu hikima yakan ƙaru da hikima,
amma abokin wawaye zai yi fama da lahani.
Faɗi 3
Kada ka yi abokantaka da mai zafin rai,
kada ka haɗa kai da wanda ba shi da wuya ya yi fushi,
in ba haka ba za ka koyi hanyoyinsa
ka kuma sa kanka a tarko.
Kowane mutum gani yake shi mai ƙauna marar ƙarewa ne,
amma ina? Da ƙyar ka sami amintacce mutum guda.
Wadata kan kawo abokai da yawa,
amma abokin matalauci kan bar shi.
Jesus, o amigo
Já não vos chamo servos, mas amigos. O maior amor é dar a vida pelo amigo. Jesus é o amigo que nunca falha.
Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana.
Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa.
Abokaina ƙaunatattu, da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ya kamata mu ma mu ƙaunaci juna. Ba wanda ya taɓa ganin Allah; amma in muna ƙaunar juna, Allah yana raye a cikinmu, ƙaunarsa kuwa ta zama cikakkiya a cikinmu ke nan.
Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin ’yan’uwanmu. In wani yana da arziki, ya kuma ga ɗan’uwansa cikin rashi, bai kuwa taimake shi ba, anya, ƙaunar Allah tana a cikinsa kuwa? ’Ya’yana ƙaunatattu, kada mu yi ƙauna da fatar baki kawai, sai dai mu nuna ta ta wurin aikatawa da kuma gaskiya.
Aka kuma cika nassin nan da ya ce, "Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne gare shi," aka kuma ce da shi abokin Allah.
Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta ’yan’uwa. Kowa yă yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.
Companheiros de fé
Dois são melhores do que um. Os companheiros de fé se fortalecem mutuamente e caminham juntos com o Senhor.
Biyu sun fi ɗaya,
gama suna samun riba mai kyau na aikinsu.
In ɗaya ya fāɗi,
abokinsa zai taimake shi yă tashi.
Amma abin tausayi ne ga mutumin da ya fāɗi
ba shi kuma da wanda zai taimake shi yă tashi!
Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma
sa’ad da ’yan’uwa suna zaman lafiya!
Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai,
yana gangarawa a gemu,
yana gangarawa a gemun Haruna,
har zuwa wuyan rigunansa.
Yana kamar raɓar Hermon
da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona.
Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa,
har ma rai na har abada.
Ni aboki ne ga duk mai tsoronka,
ga duk wanda yake bin farillanka.
Yonatan kuma ya yi yarjejjeniya da Dawuda saboda yana ƙaunarsa kamar ransa.
Kada fa a ruɗe ku, "Ajiyar mugayen abokai yana ɓata hali mai kyau."