Pular para o conteúdo
Publicidade

Zefaniya 2

1 Ku tattaru, ku tattaru,

Ya ku al’umma marar kunya,

2 kafin ƙayyadadden lokacin nan zo

ranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayi

kuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji auko muku,

kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku.

3 Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u,

ku da kuke yin abin da ya umarta.

Ku nemi adalci da tawali’u;

mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.

Hukunci a kan Filistiya

4 Za a yashe Gaza

a kuma bar Ashkelon kango.

Da tsakar rana Ashdod za zama babu kowa

a kuma tumɓuke Ekron.

5 Taku ta ƙare ku da kuke zama a bakin teku,

Ya ku mutanen Keretawa;

maganar Ubangiji tana gāba da ke,

Ya ke Kan’ana, ƙasar Filistiyawa.

"Zan hallaka ki

kuma babu abin da zai rage."

6 Ƙasar da take a bakin teku, inda Keretawa2.6 Ma’anar Ibraniyanci na wannan kalma ba ta da tabbas suke zaune,

za zama wurin da makiyaya da ta garken tumaki.

7 Za zama mallakar raguwar gidan Yahuda;

a can za su sami wurin kiwo.

Da yamma za su kwanta

a gidajen Ashkelon.

Ubangiji Allahnsu zai lura da su;

zai maido musu da martabarsu.2.7 Ko kuwa zai dawo musu da waɗanda aka kwasa zuwa bauta

Hukunci a kan Mowab da Ammon

8 "Na ji irin zagin da Mowab take yi,

da kuma ba’ar Ammonawa,

waɗanda suka zagi mutanena

suna kuma yi barazana a kan ƙasarsu.

9 Saboda haka, muddin ina raye,"

in ji Ubangiji Maɗaukaki,

Allah na Isra’ila,

"tabbatacce Mowab za zama kamar Sodom,

Ammonawa kuma kamar Gomorra,

ƙasa mai ciyayi da rammukan gishiri,

ƙasa marar amfani har abada.

Raguwar mutanena za su washe su;

waɗanda suka rage na al’ummata za su gāda ƙasarsu."

10 Wannan ne zai zama sakamakon girmankansu,

saboda zagi da kuma ba’ar da suka yi wa mutanen Ubangiji Maɗaukaki.

11 Ubangiji zai zama abin tsoro a gare su

sa’ad da ya hallaka allolin ƙasar.

Al’ummai a kowane bakin teku za su yi masa sujada,

kowa a ƙasarsa.

Hukunci a kan Kush

12 "Ku ma, ya Kushawa,2.12 Wato, mutanen da suke a yankin kogin Nilu na Bisa

za a kashe ku da takobina."

Hukunci a kan Assuriya

13 Zai kuma miƙa hannunsa gāba da arewa

kuma hallaka Assuriya,

zai mai da Ninebe kango gaba ɗaya

ta kuma zama busasshiya kamar hamada.

14 Garkuna za su kwanta a can,

da kowace irin halitta,

Mujiyar hamada da bushiya

za su zauna a kan ginshiƙanta.

Kukansu za ratsa tagogi,

ɓuraguzai za su tare ƙofofin shiga,

za a kware ginshiƙan al’ul.

15 Birnin da yake harka ke nan

da take zaune lafiya.

Ta ce wa kanta,

"Ni ce, kuma babu kamata."

Dubi irin kangon da ta zama mana,

mazaunin namun jeji!

Duk wanda ya wuce ta sai ya yi mata tsaki

yana kaɗa kai.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também

Sofonias
Ver todos os capítulos de Sofonias