Pular para o conteúdo
Publicidade

Amor ao próximo

Por Bíblia Online

O amor ao próximo não é opcional — é mandamento. Amarás o teu próximo como a ti mesmo. A lei inteira se cumpre nesta palavra. O amor ao próximo é prova do amor a Deus.

Ƙauna don abokan gāba

"Kun dai ji an faɗa, Ka ƙaunaci maƙwabcinka, ka kuma ƙi abokin gābanka. Amma ina gaya muku, ku ƙaunaci abokan gābanku kuma ku yi wa waɗanda suke tsananta muku addu’a,

Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.

Ku yi ƙauna, gama ranar ta yi kusa

Kada hakkin kowa zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Doka ke nan.

Ya kamata kowannenmu faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma gina shi.

Ku yi kome da ƙauna.

Ubangiji sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku.

Gargaɗin ƙarshe

Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar yan’uwa. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba. Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.

In fa kun kiyaye dokan nan ta mulki wadda take cikin Nassi mai cewa, "Ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka," kun yi daidai.

Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

Da yake Allah ya mai da ku zaɓaɓɓu, tsarkaka, ƙaunatattu, sai ku dinga jin tausayin juna, kuna yin alheri, kuna nuna tawali’u da sauƙinkai da jimrewa. Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku. Fiye da waɗannan duka, ku yi ƙaunar juna, gama ƙauna ce take haɗa kome gaba ɗaya.

Ku bar salamar Kiristi yi mulki a zukatanku, da yake a matsayin gaɓoɓin jiki ɗaya an kira ku ga salama. Ku zama masu godiya.

Ku ƙaunaci juna

Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.

Duk mai ƙin ɗan’uwansa mai kisankai ne, kun kuma san cewa ba mai kisankan da yake da rai madawwami a cikinsa.

Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin yan’uwanmu.

Yadda muka san ƙauna ke nan, wato, Yesu Kiristi ya ba da ransa dominmu. Ya kamata mu ma mu ba da rayukanmu domin yan’uwanmu.

Ƙaunar Allah da kuma tamu

Abokaina ƙaunatattu, mu ƙaunaci juna, domin ƙauna tana zuwa daga Allah ne. Duk mai ƙauna, haifaffe ne na Allah, ya kuma san Allah. Duk wanda ba ya ƙauna, bai san Allah ba, domin Allah ƙauna ne.

Seja o primeiro